DANGANTAKAR AURE
zainab taja dogon ajiyar zuciya ta kalleshi tace Naji nayi laifi ayi hakuri bazan sake ba zauna pls, da kyar tasamu ya zauna yana wani shan kamshi ya harde hannu tare da daura kafa daya kan daya ya bata rai..ta kallesa a zuciyarta tace yau kuma ta kaina abin ya motsa, nan ta nufi kicin ta dauko mai juice mai sanyi da cup ta ajiye a gabansa, ta tsiyaya ta mika masa ya karba kamar baya so..nan ta zauna a kujeran gefensa har ya gama sha ta kallesa...tace uncle Rufa'i (you are a gentleman) fada da ni ko sani yin karya bai dace da kai ba, in na maka laifi ko wani kuskure sai ka fada min ko in akwai abinda nake bana so sai ka fada min in gyara, amma wannan halin da kake nuna min ban kamaci haka ba ni matarkace ba kayan sawa ba da ko yaushe kakeso kasa ko ka cire kada ka maida mana rayuwar aure abin wasa
ya kafa mata idanu,sai da tasha jinin jikinta yace ke kika maida mana rayuwarmu abin wasa, dubi idona kinga nayi kama da wanda za'a yaudara? ina so ki tashi mu tafi yanzu kuma kiyi abinda na saki ba wasa, ta matso gabansa ta durkusa gami da jawo hannayensa duka ta rungume ta langabe kai cikin sanyin murya tace kayi hakuri kayi kokari ka fahimta uncle Rufa'i bazan iya zuwa inyi karya ba. Rufa'i da bana sonka da zan iya zuwa ince bana sonka ba tare da shakka ko tsoro ba, to amma ina sonka, yazanyi inyi karya? ta mike daga durkuson da tayi tare da kwanciya a jikinsa ta lumshe ido tana shakar kamshinsa sonshi na ratsata tace Rufa'i maganata kai farincikina kai, yazan iya zuwa gaban iyayenmu ince bana sonka, bayan kaine Rayuwata......
No comments:
Post a Comment