HAMSHAKIYA
Hajiya ta kalli Hamida tace kin zama uwa kina shekara sha bakwai,ko da yake uwa fa y'atace ba ke ba, saboda ko me kika haifa wani iri kika haifa ba sani zakiyi ba haka ko sunan uban yaranki ba sani zakiyi ba balle ki sanshi, komai a rufe yake bazaki taba gane wace zuri'a kika haifawa yara ba...sannan a yadda kike matsiyaciya kaskantacciya bazaki iya taba zuwa ko kusa da inda yaranki suke ba balle ubansu kina bukatar power ki kafin ki samu zuwa kusa dasu...don haka kina da zabi ko kiyarda ki manta da kin taba haifan wasu yara ki karbi ladan hayar mahaifarki da kika bayar kika haifesu...ko ki kama hanya ki tafi ko insa a fitar dake daga garin nan ta tsiya tsiya ko kina so ko ba kyaso kuma ba ko sisi ki tafi a wulakance, ki gode Allah da ya baki wannan damar dan kuwa ba ko wata mace bace tasamu damar haifa da shayar da y'ay'an (richest man) kamar sa ba, daga haifar su har an mallaka musu dukiyar da hankalinki bazai iya dauka ba...dan haka na gutsiro miki kadan daga ciki matsayinki na wacce ta bada hayar mahaifanta aka haifesu,Hamida ta runtsa ido tana jin wani irin radadi da bacin rai tare da bakin ciki suna ratsata....hawaye na zuba....
No comments:
Post a Comment