Zarah ta kalli mallam sule tana dariya tace mal sule kana ta godiya kamar wanda kake gaban gwamna din, tuni mal sule ya shiririce gaban sa na faduwa, mahmud ne ya kau da shirun ya kalli zarah yanajin wani Abu mai sanyi da dadi yana ratsashi yayi murmushi yace zarah ai mal sule baxai iya magana a gaban gwamna ba, dan kuwa idon gwamna ja ne kamar na zaki fuskarsa a daure take baya dariya, kuma bai da kyau, zarah ta zaro ido tace laaa haka yake? ai na fada maka kai kadai ne soja me kyau, ya kalleta yace nidin ina da kyau? shiru tayi ta sunkuyar da kai, shikuma yana kallonta yana murmushi yana jin kaunarta da tsantsan sonta a ransa.mal sule ne yasako baki yace yallabai gwamna fa jarumin namiji ne ga kyau ga kwarjini ga ilimi ga mulki gwamna kuma dan sarki zarah tayi carab tace duk kyansa da kwarjininsa bai kai mal mg na ba
mal sule yace ai ku mata irin yallabai kukeso kema in kinzo aure irinsa zaki zaba...ta zaro ido tare da fadin cab! ni bana sonsa in nazo aure irin ya mahammad zan zaba in aura, runtse ido yayi ya mike idonsa ya kada yayi ja kishi ya turnikeshi yaji zuciyarsa na tafasa ya mike tare da zaro kudi masu yawa ya mikawa mal sule...ya fita tuni mal sule ya tsure ya soma hango mahmud din da ya sani gwamnan kuma sojan da ba ya wasa balle dariya...fita yayi a fusace zarah ta bishi duk saurinta ta kasa kamoshi mallam mg ka jirani bazan iya saurin ka ba, bai saurareta ba, zanyi kuka fa ta fada cikin muryan shagwaba...yana jin muryanta mai hade da sonta na ratsashi amma sai ya share bai tsaya ba sai da ya isa wani dakali ya zauna...tana isowa wurin itama tayi banza dashi ta wuce bata kulashi ba, zarah! yakirata da karfi amma bata kulashi ba...mikewa yayi yasha gabanta yace zarah tafiya zakiyi kibarni? canja hanya tayi bata kulasa ba, ya sake shan gabanta zarah pls karki min haka kinaso kice baki fahimci komai ba? kanta sunkuye tace ban sani ba, kuma bana son sani kabani hanya in wuce kafin ruwa ya sauko...wucewa tayi tabarshi a wurin har ta kusa isa gida ya bita ya jawo gyalenta ya rike, cak ta tsaya..yasha gabanta zara kince bakisan me yasani fishi ba? Zarah ina neman Alfarma in kina tare dani karki sake kiran sunan yayanki zarah bazan iya jure hakan ba, bazan jure ganin wani namiji ya fini muhimmanci a rayuwarki ba, zara ina son zama wani Abu mai muhimmanci da daraja a rayuwarki. ta juyo ta kallesa ta lura gaba daya a birkice yake idonsa jawur tashin hankali bayyane karara a fuskarsa, hankalinta taji ya tashi ganinsa cikin wannan yanayi ya taba mata zuciya, amma sai ta jure tace masa..ya muhammad shine namijin da na fara rayuwa dashi kuma shine namijin da zan gama rayuwa dashi in shaa Allah...ZARAH taji ankira sunanta gabanta taji ya mummunan faduwa saboda gane muryan, ta juya da sauri muhammad ne rataye da jakarsa hannunsa rike da akwati...ya muhammad ta fada cikin daga murya da farin ciki tana oyoyo ta karbi jakarsa tana dariya...kallonta yake ya kasa magana haka ya kasa daga idonsa a kanta har ta dan soma jin kunya tace ya muhd bazaka min magana ba ko sai nakira daya sunan ME SONA yayi murmushi yace zaran ya muhd ta girma zancewa Abba yayi sauri ya aura min zara na...sunkuyar da kai tayi tana murmushi.
mahmud na tsaye yana jinsu ya kasa koda motsi balle ya daga kafa, kallo daya yayiwa muhd yaji wani irin tsanarsa da kinsa ya darsu a zuciyarsa ya juya musu baya ya dingajin kalamansu na kona masa zuciya ransa ya mugun baci hankalinsa ya mummunan tashi lokaci guda yaji duniyarsa tazo karshe...kalaman zarah suka dinga yawo a kunnensa haka dariyarta da muhammad ya kusa haukatashi kwakwalwarsa yaji tana neman juyewa komai ya cushe masa.
No comments:
Post a Comment