IGIYAR RAYUWA
shahida ta jima tana kallon hotonsa da ke manne jikin magazine din...tuni taji kuka ya kubuce mata wayyo Allah dan uwa rabin jiki jaabir dina ina zan sake ganinka? a yau idanuna da zuciyata suna matukar son ganin kanina dan uwa na jaabir dina.
jaabir din ne yashigo yana rungume da jaabir karami tare da kayan wasan sa...tayi murmushi tace dan uwa baka gajiya kayan wasa sun masa yawa, yace kyale shi ni da dana ba batun gajiya kin san son da nake wa maman sa ya shafeshi. tayi murmushi tace Dan uwa baka gajiya da son yayarka, i blieve duk duniya bazan samu me sona da kaunata irin ka ba, jaabir yanzu in akwai wanda na yadda dashi bana shakku akansa to kaine na tabbatar in ina tare da kai bazan taba bakin ciki ba, duk da ance rayuwa na tafiya tare da bakin ciki da farin ciki nasan bazan bakin ciki tare da kai ba.
ya kafa mata idanu yace kin yadda da hakan yar uwa? kwarai ta girgiza masa kai ya kalleta tare yace in fadi wani Abu? ina jinka, ya kalleta sosai yace y'ar uwa mai zai hana mu canja dangantakar mu, ban fahimce ka ba? sai da yayi dan shiru sannan yace ina nufin mubar dangantakar yaya da kani, tayi murmushi tace kana nufin kai ka dawo yaya ni kanwa? dan kawai kaga kazama kato ka fini tsayi da girman jiki ko? kar ka manta shekara bakwai nake baka, ya zuba mata idanu yace ba haka nake nufi ba...me kake fadi ne jabir nifa ban gane kan maganganun ka ba fa, saurareni yar uwa ya juya mata baya ina so dangantakar mu ya koma na aure.ina sonki yar uwa ina son aurenki.ni kadaine namijin da zai iya saki farin ciki zan nesan taki da duk wani bacin rai na rayuwa, zamu rayu cikin farin ciki ni da ke da jaabir karami.y'ar uwa a tun lokacin da na fahimci ba abin da ya hadamu bamu da dangantaka ta jini tun daga ranar (feelings) dina gareki ya canja na kasa son ko wata mace a rayuwata sai y'ar uwata yaya shahida na, ya juyo yana fadin yar uwa ki Au.....ya kasa karasawa saboda tsananin firgita,kaduwa rudani da tsantsan tashin hankali da ya shiga sanadiyar ganin halin da y'ar uwarsa ta shiga dalilin kalaman da ya furta mata a yanzu......
No comments:
Post a Comment